(ABNA24.com) A alkaluman data sabunta a shafinta na twitter, hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta kuma ce an samu karin mutum 15 da cutar ta yi jalinsu a cikin sa'o’i 24 a fadin kasar.
NCDC ta kuma ba da rahoton cewa mutum 265 sun warke daga cutar.
Najeriya dai na daga cikin kasashen Afrika inda cutar ke saurin yaduwa.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka ya haura dubu 500,000, kuma akwai damuwa yayin da karin kasashe ke fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar.
Sanarwar da hukumar ta WHO ta fidda ta ce ya zuwa yanzu, cikin kasa da wata biyar, cutar COVID-19 ta lakume rayuka kimanin 12,000, wanda har sun dara ta’asar da annobar cutar Ebola ta yi a yankin Afirka ta Yamma tsakamin shekarar 2014 zuwa 2016.
Adadin wadanda suka kamu da cutar ya linka sosai a kasashe 22 na yankin a cikin watan da ya gabata, kuma Kusan kashi biyu cikin uku na kasashen na fuskantar yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
Kasashen Aljeriya, Masar, Ghana, Najeriya da kuma Afirka ta Kudu su ne ke sahun gaba wajen yawan wadanda suka kamu da cutar a nahiyar.
342/